Tinubu  ya rantsar da Aminu Yusuf a matsayin shugaban hukumar kidaya ta kasa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da Aminu Yusuf a matsayin shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC).

An rantsar da sabon shugaban ne a yayin wani gajeren biki da akayi a zauren taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba gabanin fara taron majalisar.

A ranar 21 ga watan Oktoba ne baki dayan yan  majalisar dattawa suka tabbatar da Yusuf wanda ya fito daga jihar Niger a matsayin sabon shugaban hukumar ta NPC.

An rantsar da Yusuf tare da wasu kwamishinonin hukumar biyu ciki har da Tonga Betara wanda ya fito daga jihar Yobe.

Kafin a mika sunan nasa gaban majalisar dattawa sai da majalisar koli ta kasa da ta ƙunshi tsofaffin shugabannin kasa na Najeriya ta amince a naɗa shugabancin hukumar ta NPC.

More from this stream

Recomended