9.7 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaTinubu ya rage yawan tawagar da ke wakiltar gwamnatin Najeriya a babban...

Tinubu ya rage yawan tawagar da ke wakiltar gwamnatin Najeriya a babban taron Majalisar Dinkin Duniya

Date:

Related stories

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin ...
spot_imgspot_img

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin rage yawan wakilan Najeriya zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da ake gudanarwa a birnin New York na kasar Amurka. 

Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja yayin wani taron kwana daya da hukumar gudanarwar majalisar ta shirya wa shugabannin hukumomin gwamnati da ke karkashin sa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar mai take ‘Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cewa jami’an da ke da izinin zuwa UNGA ne kawai za su halarta.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban ma’aikatan ya ce, “A yayin zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, an tattauna kan rage tsadar harkokin mulki.  Kowa dai yana jira ya ga ko Najeriya, kamar yadda ake yi a baya, za ta tura ‘mafi girman tawaga’ zuwa UNGA.

“Daga abin da muka sani, mun san cewa wasu mutane suna amfani da damar irin waɗannan tarurrukan ƙasa da ƙasa don gudanar da harkoki na kashin kansu.

“Na samu umarni daga mai girma shugaban kasa cewa a wannan karon, za mu yi tsauri.  Idan ba ku da wani aiki a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kada ku shiga Amurka, kuma wannan umarni ne daga shugaba.”

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories