Tinubu ya naɗa sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin, Misis  Didi Esther Walson-Jack,OON   a matsayin sabuwar shugabar ma’aikata ta Najeriya.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale naɗin nata zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Agusta.

An naɗ Misis Walson-Jack  matsayin babbar sakatariya a shekarar 2017 inda kuma tayi aiki a ma’aikatu da dama-dama.

Sabuwar shugabar ma’aikatan za ta karɓi aiki ne daga shugabar ma’aikatan ta yanzu Dr. Folasade Yemi-Esan, CFR wacce za ta yi ritaya ranar 13 ga watan Agusta.

More from this stream

Recomended