Tinubu ya isa kasar Japan

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Tokyo na kasar Japan inda zai halarci taron kasa da kasa da kan cigaban Nahiyar Afirika da aka yi wa lakabi da TICAD9.

A wata sanarwa,Bayo Onanuga mai magana da  yawun shugaban kasar ya ce jirgin shugaban kasar ya sauka a kasar ta Japan da tsakar daren ranar Talata a gogon birnin Tokyo.

Tinubu zai hadu da sauran shugabannin kasashen Nahiyar Afirka da zasu halarci taron da zai gudana daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta a Pacifico Yokohama.

A cewar Onanuga,Tinubu ya samu tarba a sashen  shugaban kasa na filin jirgin saman Haneda dake Tokyo daga Hideo Matsubara jakadan taron TICAD9 dake kula da filin jirgin saman da kuma ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar da kuma wasu jami’ai daga ofishin jakandancin Najeriya.

More from this stream

Recomended