Tinubu ya isa birnin Lagos inda zai halarci taron ECOWAS

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Lagos inda zai halarci bikin cika shekara 50 na Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma wato ECOWAS.

Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad da misalin karfe 4:14 na yammacin ranar Talata.

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu tare da wasu manyan gwamnati ne suka tarbi shugaban kasar a filin jirgin.

Ana sa ran shugaban kasar tare da wasu shugabannin kasashen Afrika za su gabatar da jawabai a wurin taron.

Har ila yau shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka a ranar 31 ga watan Mayu.

More from this stream

Recomended