A ranar Lahadin ne shugaba Bola Tinubu ya isa birnin New York domin halartar manyan tarukan babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Mista Tinubu ya isa filin jirgin sama na JF Kennedy da ke birnin New York da misalin karfe 6:45 na yamma agogon kasar.
Shugaban kasar dai yana jagorantar tawagar Najeriya ne domin halartar taron da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 18 zuwa 26 ga watan Satumba wanda shi ne karon farko da zai fara aiki a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya.