Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da Ngozi Okonjo-Iweala, Darakta Janar ta kungiyar kasuwanci ta duniya WTO a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Okonjo-Iweala ta isa fadar shugaban kasa ta Villa tare da tsohon karamin ministan lafiya, Dr. Ali Pate da misalin karfe 2:50 na yammacin ranar Talata.
Kawo yanzu dai ba a san makasudin taron ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Ku tuna cewa Okonjo-Iweala a farkon watan Yuni ta gana da Tinubu a lokacin da dukkansu suka halarci taron shugabannin da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.
Okonjo-Iweala ita ce ministar kudi a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan.