
Abdulmumin Jibrin Kofa dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Kano dake wakiltar kananan hukumomin Kiru/ BebejiĀ a majalisar karkashin jam’iyar NNPP ya gana da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Jibrin na daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jamiyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso.
Ganawar ta su na zuwa ne yan
kwanaki bayan Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita yankin kudu wajen yin ayyukan raya kasa.
Jibrin ya yi magana da yan jaridu bayan ganawar inda ya ce ta mayar da hankali kan hadin kai da cigaban kasa.
Ziyarar na zuwa ne dai-dai lokacin da ake cigaba da rade-radin yiyuwar zama inuwa daya tsakanin Kwankwaso da Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Da aka tambaye shi ko ziyarar wani bangare ne na shirin komawa jam’iyar APC,Jibrin ya ki bayar da amsa kai tsaye amma ya ce ” Komai da komai a bayyane yake kuma mai yi yuwa ne,”