Tinubu ya fara ziyarar aiki a birnin Maiduguri

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno inda zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Babagana Umar Zulum ya aiwatar.

Ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da makarantu, motoci masu aiki da lantarki da kuma wasu ayyuka da Zulum ya aiwatar da hadin gwiwar gwamnatin tarayya..

A ranar Juma’a ne mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya sanar cewa shugaban kasa , Tinubu zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a jihohin Borno da Bauchi da kuma Lagos daga ranar Asabar.

Ya kuma ce shugaban kasa zai halarci daurin auren Sadeeq Sherif dan gidan tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff

Daga Maiduguri shugaban kasar zai wuce Bauchi inda zai yiwa gwamnatin jihar da iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi taaziyar rasuwar shehun Malamin.

Bayan ya gama da Bauchi ne zai wuce birnin Lagos inda zai yi hutun bikin Kirsimeti a can.

More from this stream

Recomended