
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar aiki da ya kai kasashen Brazil da kuma St. Lucia dake yankin Karebiyan.
Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da tsakar daren ranar Asabar.
Tinubu ya samu tarba daga ministan tsaro, Bello Matawalle, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, Sanata Aliyu Wamako, mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da kuma Ibrahim Masari Mai bawa shugaban kasa shawara, kan harkokin siyasa.