
Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan da ya halarci taron shugabannin Afirika kan makamashi da aka yi a birnin Daresalam na ƙasar Tanzania.
Shugaban kasar ya bar gida Najeriya a ranar Lahadi domin halartar taron da aka yi daga ranar 27 zuwa 28 na watan Janairu.
Tun da farko mai magana da yawun shugaban ƙasar,Bayo Onanuga ya ce shugabannin ƙasashen Afrika, na kamfanonin masu zaman kansu da kuma kungiyoyin bayar da tallafi dama masu zaman kansu za su tattauna kan hanyar da za gaggauta samar da makamashi a faɗin nahiyar.
Gwamnatin Tanzania da haɗin gwiwar Bankin Duniya da Bankin Raya Ƙasashen Afrika ne suka ɗauki nauyin taron.
Tinubu wanda ya sauka da daddare a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati.
A cikin waɗanda suka tarbi shugaban akwai shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, Nuhu Ribadu mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da kuma ministan tsaro, Bello Matawalle.