Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Birtaniya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan da ya shafe mako biyu yana hutu a Birtaniya.

Shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Abuja da maraicen ranar Asabar.

Olusegun Dada mataimakin shugaban ƙasa musamman kan soshiyal midiya shi ne ya sanar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne shugaban ƙasar ya sanar da cewa zai fara gudanar da wani hutu na makonni biyu.

Bayan kwanaki 10 ne mai bawa shugaban ƙasar shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Masari ya sanar da cewa Tinubu zai ta fi birnin Paris na ƙasar Faransa daga London.

A ranar Laraba ne mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya sanar da tafiyarsa ƙasar Sweden inda ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

More News

APC ta lashe zaben kujerun ƙananan hukumomi da kansilolin jihar Kaduna

Jam'iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kaduna 23 da kuma na kejerun kansilolin jihar. Hajara Muhammad shugabar hukumar zaɓe mai zaman...

An sallami Æ´an sanda uku daga bakin aiki kan kisan wani dalibi

Rundunar Æ´an sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami'an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya...

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da Æ´an ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an Æ´an sanda da kuma sojoji suna É—aukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...