
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar da yakai birnin Rome na kasar Italiya inda ya halacci bikin kaddamar da Fafaroma Leo XIV.
Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 6:50 na yamma.
Tinubu ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da kuma shugaban jam’iyar APC na kasa, Abdullah Umar Ganduje.
Shugaban kasa ya bar Abuja a ranar Asabar biyo bayan gayyatar da aka yi masa ta halartar bikin kaddamar da Fafaroma Leo XIV.