Tinubu ya dakatar da gwamnan babban Najeriya Emefiele

Shugaba Bola Tinubu ya amince da dakatar da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya.

Daraktan ofishin yada labarai na sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ne ya bayyana hakan a cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa a daren Juma’a.

Ya bayyana cewa yana mayar da martani ne ga wani bincike da ofishinsa ke gudanarwa da kuma sake fasalin fannin hada-hadar kudi da ke tafe.

An umurci Emefiele da ya gaggauta mika ragamar tafiyar da harkokin ofishinsa ga mataimakin gwamna (Operations Directorate), wanda zai yi wannan aiki har sai an kammala bincike da sauye-sauye.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...