Tinubu ya bukaci ƴan Najeriya da su nuna goyon bayansu da yaƙi da miyagun kwayoyi

Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba ya bukaci ‘yan Najeriya da su nuna goyon bayansu da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, a wani shiri na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Shugaban wanda sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya wakilta a taron, ya ce wannan goyon bayan ya zama dole domin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a kasar.

A yayin bikin ranar yaki da shan muggan kwayoyi da safararsu ta duniya, wadda aka sa a ranar Laraba 26 ga watan Yuni 2024, a dakin taro na fadar gwamnatin tarayya Abuja, Tinubu ya tabbatar wa hukumar yaki da muggan kwayoyi goyon bayan gwamnatinsa.



“Ina kira ga kowa da kowa da su goyi bayan shirin yaki da shan miyagun kwayoyi, wanda aka fi sani da yakin WADA, wanda NDLEA ta kaddamar shekaru uku da suka gabata.  Ina yabawa kuma ina kira ga kowa da kowa da ya rubanya kokarinsa na yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan,” inji Tinubu.

More News

Sojoji sun kama ƴan bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu ƴan bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Sojoji sun kama ƴan bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu ƴan bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutun bikin samun ƴancin kai

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ƴan cin...

Jami’an EFCC sun kai samame gidajen kwanan ɗaliban UDUS

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kai wani samame da tsakar dare a kan gidajen kwanan dalibai na...