Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin  gaggauta sakin yaran nan da aka gurfanar a gaban kotu inda ake tuhumarsu da zargin cin amanar ƙasa.

Ministan yaɗa labarai, Muhammad Idris shi ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin a fadar shugaban ƙasa.

Ya ce shugaban kasar ya bawa ministan shari’a, Lateef  Fagbemi umarnin gaggauta sakin yaran wadanda aka kama su a watan Agusta lokacin zanga-zangar #Endbadgovernance da aka gudanar a watan Agusta.

“Dukkansu ƙananan yara ne. Shugaban ƙasa ya bada umarnin a saki dukkanninsu,”ya ce.

“Na tuna nayi wata gajeriyar tattaunawa da shugaban ƙasa da maraicen nan ya kuma bada umarnin gaggauta sakin dukkanin yaran da rundunar ƴan sandan Najeriya ta  kama  ba tare da gindaya duk wani sharaɗin shari’a ba ,” Idris ya ce.

Shugaban kasar ya kuma umarci ma’aikatar jin ƙai da ta kula da walwalar yaran tare da tabbatar da cewa an mayar da su gaban iyayensu.

Har ila yau shugaban ƙasa ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan waɗanda suka kama tare da tsare yaran.

More from this stream

Recomended