Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanar da ƙirƙirar ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi.
Tinubu ya sanar da kafa sabuwar ma’aikatar a wurin ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan sauya yadda ake kiwon dabbobi.
Ya ce nan gaba kaɗan za a sanar da sabon ministan da zai jagoranci ma’aikatar.
Shugaban ƙasar ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasar domin shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya da kuma bunƙasa kiwon dabbobi da kuma samar da madara.
Tinubu ya kafa kwamitin ne bayan da ya karɓi rahoton taron ƙasa da aka gudanar kan sauya fasalin kiwon dabbobi da kuma magance rikicin dake tattare da kiwon.
Ya ce kwamitin zai yiddr aiki da ma’aikatar noma da wadata ƙasa da abinci domin fito da mafitar magance rikicin da ya ɗauki tsawon shekaru.