Tinubu ya ƙirƙiri sabuwar ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanar da ƙirƙirar ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi.

Tinubu ya sanar da kafa sabuwar ma’aikatar a wurin ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan sauya yadda ake kiwon dabbobi.

Ya ce nan gaba kaɗan za a sanar da sabon ministan da zai jagoranci ma’aikatar.

Shugaban ƙasar ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasar domin shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya da kuma bunƙasa kiwon dabbobi da kuma samar da madara.

Tinubu ya kafa kwamitin ne bayan da ya karɓi  rahoton taron  ƙasa da aka gudanar kan sauya fasalin kiwon dabbobi da kuma magance rikicin dake tattare da kiwon.

Ya ce kwamitin zai yiddr aiki da ma’aikatar noma da wadata ƙasa da abinci domin fito da mafitar magance rikicin da ya ɗauki tsawon shekaru.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...