Tinubu Na Cikin Koshin Lafiya Bayan Tuntuɓe A Ziyararsa Ta Turkiyya



Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na cikin koshin lafiya bayan tuntuɓen da ya yi a yau Talata yayin wata faretin tarba da aka shirya masa a fadar shugaban Turkiyya da ke Ankara.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Suday Dare, ya tabbatar da cewa tuntuɓen bai jawo wa Tinubu wani rauni ba.

Tinubu mai shekara 73, ya halarci bikin tarba ne tare da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, inda aka yi masa gagarumar tarba.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na shugaban Turkiyya ya nuna lokacin da Tinubu ya yi tuntuɓe ya faɗi ƙasa, sannan jami’ai suka yi gaggawar kai masa ɗauki bayan ya kammala wucewa gaban jerin sojoji da manyan baki. Daga baya kuma an ga shugaban Najeriyar tare da Erdogan suna tattaunawa.

Rahoton ya ce an riƙa yaɗa hotuna da bidiyon lamarin a shafukan sada zumunta, lamarin da ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen Najeriya.

More from this stream

Recomended