Sanata, Eyinnaya Abaribe ɗan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Kudancin Abia a majalisar ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmad bai nemi amincewar majalisar dattawan ba kafin ya sayo sabon jirgin saman da yake amfani da shi .
Abaribe ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ake tattaunawa da shi a cikin shirin Siyasa Ayau na gidan talabijin na Channels.
Ya ce an amince da buƙatar sayen sabon jirgin ne ba tare da saninsa ba.
Sanatan ya ce yawancin manufofi da tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa Tinubu baza su iya inganta rayuwar ƴan Najeriya ba inda ya ƙara da cewa babu alamar sauƙi na zuwa anan gaba.
Ya ƙara da cewa duba da halin da ƴan Najeriya suke ciki bai kamata ace gwamnatin ta sayo sabon jirgin ba.