Mako guda bayan ya dawo daga tafiyar ziyarar da yakai ƙasar, Faransa, shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya fara shirye-shiryen tafiya zuwa ƙasar China.
A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale tafiyar shugaban ƙasar zuwa ƙasar China za ta gudana ne a makon farko na watan Satumba.
Ngelale ya ce ziyarar zuwa ƙasar China na daga cikin irin ƙoƙarin da gwamnati mai ci take na inganta rayuwar ƴan Najeriya.
A yayin da yake can ana sa ran shugaban ƙasar zai gana da shugaba Xi Jinping na ƙasar China inda za su rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi.
Har ila shugaban ƙasar zai gana da wasu shugabanni 10 na wasu manyan kamfanonin ƙasar da suka yi fice a fannin albarkatun mai da iskar gas, noma, kimiyar sararin samaniya da sauransu.