Tashin hankalin dana shiga bai misaltuwa — Zainab Aliyu | BBC Hausa

Mafi yawan `yan Adam na da burin su yi nisan kwana a rayuwa.

Wannan ne ya sa mutane kan shiga tashin hankali a duk lokacin da suka tsinci kansu a wani yanayi da za su iya rasa ransu.

Irin halin da Zainab Aliyu wata `yar Najeriya da aka zarga da safarar miyagun kwayoyi ta samu kanta kenan a kasar Saudiyya, wadda mahukunta suka sake ta bayan bincike ya gano cewa cusa mata magungunan aka yi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Najeriya.

Ibrahim Isa ya samu tattaunawa da ita a kan irin kalubalen da ta fuskanta a lokacin da aka tsare ta, Amma ya fara ne da tambayarta yadda lamarin ya faru har aka kai ga kama ta.

More from this stream

Recomended