Tarihin sabuwar ministar kudin Nigeria

Mrs Zainab Shamsuna Ahmed

Shugaban Najeriya Muhammafdu Buhari ya nada Mrs Zainab Shamsuna Ahmed a matsayin mai rikon mukamin ministar kudin kasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina ya fitar ya ce Mrs Ahmed za ta soma aiki ne ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba.

An nada a kan mukamin ne bayan saukar Mrs Kemi Adeosun sakamakon zargin yin cogen takardar hidimar kasa.

Mrs Ahmed ce karamar minista a ma’aikatar kasafin kudin kasar gabanin nadin nata.

Tarihin Zainab Ahmed a takaice

  • An haife ta a 1960 a jihar Kaduna
  • Ta yi digiri na daya a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
  • Ta yi digiri na biyu a Jami’ar jiha ta Ogun da ke Ago-Iwoye
  • Ta shafe fiye da shekara 28 tana aiki a fannin harkokin kudi
  • Ta shugabanci hukumar Nigerian Extractive Industries Transparency Initiative, NEITI.
  • Ita ce karamar minista a ma’aikatar kasafin kudi

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...