Bullar annobar coronavirus a duniya a wannan karni da irin barnar da take yi suna tayar da hankulan jama’a da dama.
Duniya ta jima ba ta ga wani lamari da ya rikita kowa ba, ya kuma jefa fargaba da rudu a duk sassan duniya kamar abin da coronavirus ko covid-19 ta haifar.
Sai dai har yanzu a Najeriya dumbin mutane ne ke da shakku ko ma kin yarda da cewa cutar gaskiya ce.
Duk kuwa da irin yadda take barna da tsayar da al’amura a kasashen duniya da kuma yadda tuni ta shiga Afirka da Najeriyar ma.
Cikin masu kin yarda da gaskiyar cutar kuwa har da malaman addini na Musulunci da na Kirista, inda wasu ke ta fada wa mabiyansu cewa kirkirar cutar aka yi don yi addinai makarkashiya.
Sai dai kwararru a fannin lafiya na ta jan hankulan jama’a cewa dole su kula tare da daukar matakan kariya ganin yadda cutar ke barna a wasu kasashen duniya, don kuwa gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
An sha samun annoba daruruwan shekaru da suka gabata a duniya, wadanda har gobe ana tuna illar su a tarihi.
- Coronavirus: Kai tsaye, alkaluman cutar a Afirka
Misali ko a tarihin Musulunci, malamai da dama sun ambato cewa a lokacin mulkin Sayyadina Umar, wato halifa na biyu bayan Manzon Allah SAW an yi wata annoba da ta zama ajalin Sahabbai, inda suka yi ta mutuwa, ciki har da irin su Abu Ubaidah Bn Jarrah da Mu’adh bin Jabal.
”Sannan ko a 1215 an samu barkewar wata annobar a Masar da Sham da Falasdinu, wadda sai da kusan rabin al’ummar wadannan yankuna suka mutu,” kamar yadda babban limamin Masallacin Kasa na Najeriya da ke Abuja Farfesa Ibrahim Maqary ya fada a wajen wani karatunsa.
A tarihin duniya baki daya ma dai an taba samun manyan annoba da suka dauki rayukan jama’a bila adadi kuma suka durkusar da al’amura.
Farfesa Isa Sadiq Abubakar, darakta na cibiyar bincike mai zurfi kan cutukan da ke yaduwa a Jami’ar Bayero Kano ya shaida wa BBC cewa ”akwai cutar da aka yi annobarta shekaru aru-aru mai suna Plague wadda ta kashe kusan rabin al’ummar Turai a 1343.
Sannan a baya-bayan nan ma an sha fama da annobar cutar Ebola a duniya, inda ta kashe mutane da dama a wasu kasashen Afirka a tsakanin 2014 zuwa 2015.
Baya ga wadannan, akwai annoba da dama da aka yi fama da su musamman a arewacin Najeriya a shekaru da dama da suka gabata, kuma har a shekarun baya-bayan nan ma wasu na kara tasowa akai-akai.
A cikin wannan makala, mun yi waiwaye kansu ta hanyar tuntubar kwararru a fannin lafiya:
Spanish Flu
Wannan wata mummunar annoba ce da ta shafi duniya baki daya a 1918 wadda ta kashe kusan mutum miliyan 50.
”Kuma ta shiga har Najeriya da ma arewa,” a cewar Farfesa Abdussalam Nasidi, tsohon shugaban Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC.
”A lokacin da annobar ta barke yawan al’ummar Najeriya ya kai miliyan 40, kuma mutum miliyan 20 ne suka kamu a kasar, sannan mutum 500,000 suka mutu.
”Annobar ta kai wata shida tana addabar mutane kuma ta yi ta yaduwa ne ta hanyar shiga da fitar da aka dinga yi tsakanin kasashe ta jirgin ruwa, abin da ya zama sanadin yaduwarta a duniya,” in ji kwararren.
A lokacin da annobar ta addabi duniya babu ci gaban kimiyya kamar yanzu don haka an sha wahala wajen dakile ta.
Sankarau
Wannan cuta ce da duk wanda ya kwana ya tashi a arewacin Najeriya ya san da ita. Kuma har a baya-bayan nan ba ta daina addabar al’ummar yankin ba.
Farfesa Nasidi ya ce ko a shekarun 1996 da 1997 annobar sankarau ta yi munin da sai da ta hallaka mutum 11,000 a Kano kawai.
Farfesa Isa Sadiq ya kara da cewa “A da idan aka yi annobar da ta dauki ran mutane da yawa sai kuma ta lafa sai bayan wasu shekarun. Tun daga 1996 ba a kara samun mummunar annobar sankarau ba sai wajen 2015.”
Baya ga kisa da sankarau ke yi, Farfesa Isa ya ce tana makantar da mutane, ta kurmantar ko ta bata kwakwalwar wasu.
Amai da gudawa (Kwalara)
Cutar amai da gudawa na daga cikin annobar da suka dinga addabar jama’a a arewacin Najeriya. Sannan annoba ce da kan taso lokaci zuwa lokaci.
Farfesa Isa ya ce “An fi samun ta a lokacin rani idan ruwa ko abinci ya gurbata. Kuma ta kan kashe mutane.
”Ana samun annobar kwalara shekaru da dama da suka gabata tun gabanin kafa Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO. A kan samu bullar annobar lokaci zuwa lokaci a duniya baki daya.
”Hasali ma bayan an gama Yakin Duniya Na II hukumar da ke kula da matsalolin lafiya ta duniya ta wargaje. Don haka sai aka kafa WHO, kuma aikin da ta fara yi a lokacin da aka kafa ta shi ne kokarin dakile annobar kwalara da ta mamaye duniya.
Sai dai a kasashe irin namu da ba su ci gaba ba har yanzu a kan samu bullar kwalara nan da can saboda matsaloli da suka hada da kazanta.
Kyanda
Wannan wata annoba ce da ta fi addabar yara kuma aka dade ana fama da ita a duniya.
Daga baya duk kasashen duniya kusan sun shawo kanta, sai dai har yanzu a Najeriya musamman yankin arewaci, tana ci gaba da tasowa lokaci zuwa lokaci.
Farfesa Abdussalam Nasidi ya ce: ”Duk da cewa annobar kyanda ta ki ci ta ki cinyewa a arewacin Najeriya, amma ta fara raguwa duk da yake ta yi barna sosai a baya.”
Agana
Duk wanda ya kai shekara 60 ko ya haura matukar dai a arewacin Najeriya yake to ya san annobar cutar agana.
A lokacin da ta bulla, ta yi tsanani a yankin kuma ta yi barna sosai. Sai dai daga baya an samar da riga-kafinta kuma an kawar da ita dungurungum.
Farfesa Nasidi ya ce: ”Likitocin Najeriya na daga cikin wadanda suka taimaka sosai aka kawar da ita a duniya baki daya.”
Rufewa
Farfesa Isa Sadiq ya ce ko annobar koronabairus ta wuce, hakan ba yana nufin duniya ta koma ta nade hannu ba ne, ba tare da shirya wa tunkarar wata annobar nan da wsu shekarun ba.
”Wannan ba ya nuna cewa iyakar ta kenan, dole dan adam ya zauna da shirin cewa za a iya samun annoba. Ai yanzu wasu masanan na nuna cewa ita coronavirus ai ‘yar uwar SARS ce ta sauya yanayinta.
Da ma haka kwayoyin cuta suke, muna shiri su ma suna mana mummunan shiri. Sai ta sauya yanayinta ta fi karfin wadda ta zo ta buwayi mutane.
Alal misali ai ita SARS an sha kanta cikin sauki, amma wannan coronavirus ai ta buwayi mutane. Kalli yadda take wahalar da kasashe masu karfin tattalin arziki da ci gaban kimiyya da fasaha irin su Amurka da China da Jamus da Burtaniya da Spain, duk abin na fin karfinsu.
”To mu a nan Najeriya abuuwan sun fi muni. Mutanenmu ba sa jin magana. Duk abin da aka hana ba sa hanuwa,” in ji Farfesa Sadiq.
”Sannan wasu gwamnatocinmu suna da tausayi, yanzu kuma ba lokaci ne na tausayi ba, kamata ya yi a yi aiki da karfin iko a hana mutane fita,” in ji farfesan.
Karin labarai masu alaka