
Wata motar tanka dake dauke da man fetur lita 45,000 ta yi bindiga a ranar Litinin bayan da tafadi akan titin Iseyin -Oyo a karamar hukumar Iseyin ta jihar Oyo a karo na biyu cikin kasa da sati biyu.
Motar mai rijistar namba Lagos LM 62 XP an rawaito ta kwace daga hannun direban ta fada rami ta kama da wuta.
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Maroof Akinwade ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Ibadan babban birnin jihar.
Ya ce hukumar ta samu kiran kai daukin gaggawa da karfe 10:46 na safe inda jami’an kashe gobara karkashin jagorancin PFS1 Azeez suka garzaya wurin.
Sanarwa ta ce jami’an sinyi amfani da sinadari mai kumfa wajen shawo kan gobarar.