Tambuwal da magoya bayansa 10,000 sun fice daga jam’iyar PDP ya zuwa APC

[ad_1]
Abubakar Shehu Tambuwal , tsohon shugaban jam’iyar PDP a jihar Sokoto ya fice daga jam’iyar ya zuwa APC tare da magoya bayansa 1000.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, Shehu Tambuwal ya ce sun yanke shawarar ne a kashin kansu ta yin siyasa domin kawo cigaba mai amfani ga jama’a.

Ya ce sun gamsu su koma jam’iyyar ne saboda tsare-tsare masu kyau da kuma aiyukan cigaba da gwamnatin jam’iyar APC ke gudanarwa inda ya kara da cewa kamata ya yi dimakwaradiya ta zamo hanyar samar da abubuwan more rayuwa da kuma cigaban jama’a.

Shehu Tambuwal ya kuma taba riƙe muƙamin kwamishinan ilimi a jihar.

Umar Maitafsir, shugaban jam’iyar APC reshen karamar hukumar Tambuwal ya ce akalla mutane 100,000 daga kananan hukumomin Yabo, Kebbi, Ture ta,Dange/Shuni, Bodinga da kuma Shagari sun fice daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.
[ad_2]

More News

NDLEA ta kama tan 761,000 na miyagun kwayoyi cikin shekaru 3

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi...

An saka jirage uku na  shugaban ƙasa a kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen...

Ƴan bindiga sun kashe mai POS a Ekiti

Wasu ƴan bindiga sun kashe wani mai sana'ar POS a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti. Mai sana'ar ta POS dake da suna Alfa Taofeek...

Har yanzu Sanusi ne sarkin Kano—Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta yanke a safiyar ranar Alhamis...