Taliban ta tsagaita wutar kwana uku don bikin Ƙaramar Sallah

Afghan troops

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An samu Æ™aruwar kai hare-hare kan dakarun gwamnati a ‘yan makwannin nan

Ƙungiyar Taliban ta ba da sanarwar tsagaita wutar kwana uku da gwamnatin Afghanistan wadda za ta fara aiki daga ranar Ƙaramar Sallah a Lahadin nan.

Matakin na zuwa ne bayan Æ™aruwar hare-hare daga Æ™ungiyar ‘yan ta-da-Æ™ayar-baya masu tsattsauran ra’ayi kan dakarun gwamnati cikin makwannin baya-bayan nan.

Shugaba Ashraf Ghani ya yi maraba da sanarwar, kuma ya ce sojojinsa za su mutunta sharuÉ—É—an wannan yarjejeniya.

Yarjejeniyar ta tsawon kwana uku mai yiwuwa ne ta haɓɓaka fatan raguwar ayyukan tarzoma na tsawon lokaci a ƙasar.

Sai dai ba a iya tsawaita wata makamanciyar wannan yarjejeniya da aka cimma saboda sallar idi ba a shekara ta 2018.

“Kada ku kai duk wani hari kan abokan gaba a ko’ina. Amma idan maÆ™iya sun auka muku, to ku kare kanku,” Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana ranar Asabar.

Ya ƙara da cewa an ayyana yarjejeniyar ce taƙamaiman don bikin Sallar Idi, wanda ya kawo ƙarshen watan Ramadan mai tsarki.

“Ina maraba da wannan sanarwa,” Shugaba Asharaf Ghani ya wallafa a shafinsa na Tiwita jim kaÉ—an kuma. “Na umarci [dakarun soji] su yi aiki da yarjejeniyar ta kwana uku amma su kare kansu matuÆ™ar an kai musu farmaki.”

Al’ummar Afghanistan da masu sanya na Æ™asashen duniya sun yi fatan ganin an rage tarzoma tsakanin É“angarorin biyu sakamakon sanya hannu kan yarjejeniyar janye dakaru da Æ™ungiyar Taliban ta cimma da Amurka a watan Fabrairu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Jami’ai kaÉ—an ne a Æ™ungiyar tsaro ta Nato ke jin cewa tsagwaron Æ™arfin soja na iya yin nasara a kan Taliban

Sai dai an gamu da cikas kan batun ci gaba da Æ™arin tattaunawa game da musayar fursunoni, yayin aka samu Æ™aruwar hare-hare kan dakarun gwamnati cikin ‘yan makwannin nan.

Wani hari da aka kai kan wani asbitin haihuwa da ke babban birnin ƙasar, Kabul a farkon wannan wata ya janyo tofin Allah tsine daga ɓangarori da dama.

Yayin da Taliban ta musanta hannu a hari, lamarin ya harzuÆ™a Shugaba Ghani har ya ba da umarnin ci gaba da kai hare-hare kan Æ™ungiyar da ma sauran ‘yan ta-daÆ™ayar-baya.

Ya zargi masu gwagwarmaya da makamai da bijirewa kiraye-kirayen da aka sha yi don taƙaita ayyukan tarzoma.

A watan jiya, sai da Taliban ta yi watsi da wani kiran gwamnati na a tsagaita wuta a faÉ—in Afghanistan don martaba watan Ramadan.

Suka ce “babu hankali” cikin lamarin maimakon haka suka Æ™ara yawan kai hare-hare kan dakarun gwamnati.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka É—inka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an Æ´an sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello É—an...