Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. Ahmad

Ba tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura mutunci ce, ka mutunta kanka da kyau, kada sutura ta sanya a raina ka.

Wanka ko da Dudu Osun ne zai fitar maka datti, ba sai ka sayi sabulun ₦2k+ ba, Nivea ko shower gel mai tsada. Tsamin jiki zai zubar maka ƙima fiye da tunani. Alola da yawan shan ruwa suna taimakawa wajen tsare jiki daga tsami.

Ba lalle sai ka sayi turare ko body spray, ko deodorant mai shegen tsada ba, ɗan Lovelia (Gelly Cologne) na ₦500, ko body spraye Chellenge na ₦500 zuwa ₦1k za su sanya jikinka ƙamshi. Ko kuma ka tare mai turare, ka bashi ₦200 ya ɗura turare a kwalba, Fawakiha, Oud, X, Naseem, Zamzam… wani turaren na ₦200 sai ya yi maka sati guda. Ga rollers na Almas ƙasa da ₦1k.

Ba lalle sai ka sayi babban toothpaste (maclean) ba, ko ba ka da kuɗi, ka sayi asiwaki, idan ba ka da kuɗi aswaki ₦50 ko ₦100, karyi itacen darbejiya ka goge baki. Akwai ƙasƙacin kana magana bakinka na wari.

Nawa ake siyar da matajin kai (rattail comb)? Akwai na ₦100 ma. Nawa ake siyar da nailcutter? ₦100, ₦200… sun ishe ka. Dutsine goge kaushi kam kyauta ma sai ka sami, a kasuwa ba ya wuce ₦50, ₦100.

It doesn’t matter a wane irin gini kake rayuwa, na laka ne (mud), ko ginin zamani ginin siminti, ka tsaftace muhallinka, ka share, ka gyara kaya komai a muhallinsa (kada ka yi baƙo ka ji kunya). Banɗakinka ko wane iri ne, ka gyara, ka hana shi zarni da bashi maras daɗi. Kayan ƙamshi kuwa, ko tsintsiyar ƙamshi (incense) ta ₦200 kusan tsinke 20 ce, kai ma ka ji kana rayuwa, ba wai sai ka tara abin duniya ba za ka yi tsaftsaf.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #Tsafta

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa ɗansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...