Ta leƙo ta koma wa Tottenham a hannun West Ham

West Ham celebrate

Tottenham ta ga ta leko ta koma a karawar da ta yi a gida da West Ham United a gasar Premier League karawar mako na biyar ranar Lahadi.

Tottenhma ce ta fara cin kwallo uku tun kan hutu ta hannun Heung-min Son da ya ci a mintin farko daga take leda.

Harry Kane ne ya ci na biyu a minti takwas ana wasa ya kuma kara na uku na kuma biyu da ya ci a fafatawar minti takwas tsakani.

West ham ta fara farke kwallo ne ta hannun Fabian Balbuena, sannan Davinson Sanchez ya ci gida wato Tottenham daga nan West ham ta kara samun kwarin gwiwa saura minti biyar a tashi karawar.

Gareth Bale ya shiga wasan daga baya kuma a karon farko da ya koma Tottenham don buga wasannin aro daga Real Madrid, ya kuma samu damar cin kwallo amma ya barar.

Kadan ya rage Kane ya ci ta uku rigis a wasan, bayan da ya buga kwallo ya bugi turke, daga nan kuma Tottenham ta rage sa kaimi karawar tana cin 3-2.

Daf da za a tashi ne West Ham ta yi bugun tazara kuma kwallo ta je gidan Tottenham daga baya ta nufi wajen Manuel Lanzini, shi kuwa bai ba ta lokaci ba ya buga ta fada raga.

Da wannan sakamakon Tottenham tana nan a matakinta na shida ita kuwa West Ham ta yi sama kadan zuwa matsayi na takwas a kan teburin gasar Premier League ta bana.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...