Sunusi zai iya zuwa ko’ina har da birnin Kano—El-Rufai | AREWA News

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru el-Rufai ya ce tsohon sarkin Kano, Muhammad Sunusi zai iya zuwa duk inda yake so a Najeriya ciki har da jihar Kano.

Bayan da aka tube shi daga Sarkin Kano akwai rahotonnin dake cewa baza a kyale shi ya shiga Kano ba har sai bayan watanni uku.

Amma da yake amsa tambayoyi daga yan jaridu a garin Awe dake jihar Nasarawa ranar Juma’a,gwamnan ya ce babbar kotun birnin tarayya dake Abuja ta yanke hukunci cewa Sunusi zai iya zuwa duk inda yake so.

Gwamnan ya kara da cewa hukuncin da kotun ta yanke ya nuna cewa tsarewar da aka yi masa ta saba ka’ida.

“Zai iya rayuwa duk inda yake so har da birnin Kano idan yana so.Amma yanzu muna kan hanyar zuwa Abuja akwai yiyuwar Sarkin zai wuce Lagos inda tun farko ya zaba ya zauna,” el-Rufai ya ce.

More from this stream

Recomended