Sulli Deal: Manhajar da ake sanya mata Musulmai domin sayarwa

  • By Geeta Pandey
  • BBC News, Delhi
Hana Khan

Asalin hoton, Hana Khan

Bayanan hoto,
Hana Khan matukiyar jirgin sama ce wadda aka yi gwanjonta ta intanet a Indiya ba tare da saninta ba

Ranar Lahadin makon jiya, gwamman mata Musulmai a Indiya suka gane cewa an sanya tallar sayar da su a shafin intanet.

Daya daga cikinsu mai suna Hana Khan wadda matukiyar jirgin sama ce da sunanta ya bayyana a jerin wadanda za a sayar, ta shaida wa BBC cewa wata kawarta ce ta ankarar da ita ta hanyar sakon Twitter.

Sakon ya kai ta wani shafi mai suna “Sulli Deals”, wata manhaja ta intanet da ake wallafa hotunan mata daban-daban da aka bayyana su a matsayin kasuwanci.

Manhajar na dauke da hoton wata mace da ba a san da ita ba a matsayin wadda ta kirkireta. A shafi na biyu, Mis Khan ta ga hoton kawayenta, bayan wannan shafin sai kuma ta ci karo da nata hoton.

“Na kirga sunayen mata 83, watakil ma sun fi hakan. Sun dauki hotona daga shafina na Twitter, wanda ke dauke da sunan da nake amfani da shi. Kuma manhajar ta shafe kwana 20 da kirkira amma sam ba mu da labari, lamarin ya sanyaya min gaɓɓai,” inji Hana.

Manhajar ta bagarar da masu amfani da ita, ta hanyar cewa za su taimaka wa mutane sayen abin da suke so.

“Sulli” – wata kalma ce da mabiya addinin Hindu masu tsaurin ra’ayi ke kiran mata Musulmin Indiya. Babu wata shaida da ta nuna an yi cinikin wata mace, alamu sun nuna an kirkiri manhajar ne da nufin tozartawa da cin mutum matan.

Mis Khan ta ce ta san an sanya tallanta ne saboda addininta. “Ni Musulma ce wadda ake jin muryata, so suke yi su rufe mana baki.”

Shafin intanet na GitHub -wanda ya ba da damar bude manhajar ya yi saurin rufe ta bayan samun korafe-korafe. “Mun dakatar da masu amfani da manhajar bayan gudanar da bincike, saboda korafin da muka yi ta samu kana abin da ake yi da manhajar, wanda ya saba wa dokokinmu,” inji sanarwar da GitHub ya fitar.

Sai dai lamarin ya darsa tsoro a zukatan matan. Saboda wadanda aka wallafa a shafin baki daya mata Musulmai ne da ake jin muryoyinsu, sai kuma ‘yan jarida da masu fafutuka da masu bincike da sauransu.

Daidaiku daga cikinsu, tuni suka rufe shafukansu na sada zumunta, yawanci kuma sun bayyana tsoron kar a kara cin zarafinsu.

“Duk karfi da kwarin gwiwar da kake da shi, matukar aka wallafa hotonka da bayananka na sirri a bainar jama’a, dole za ka shiga damuwa da firgici,” kamar yadda wata Musulma ta shaida wa Sashen BBC Hindi.

Sai dai a wani bangaren, wasu daga cikin matan da aka wallafa hotunansu sun shiga shafukan sada zumunta tare da shan alwashin daukar mataki.

Da yawa sun samar da wata kungiya a dandalin WhatsApp, inda suke yi wa takwarorinsu tayin taimakawa musamman ga wadanda suka shiga matsananciyar damuwa, cikinsu har da Mis Khan wadda ta shigar da korafi ga ‘yan sanda.

Su ma manyan mutane da masu fafutuka ba a bar su a baya ba wajen yin Allah-wadai da cin zarafin da aka yi wa matan. ‘Yan sanda sun ce sun fara gudanar da bincike, sai dai sun ki fadin ainahin wadanda suka samar da manhajar.

Wadanda suka kirkiri manhajar dai sun yi amfani da suna da bayanan bogi, to amma Hasiba Amin wata kwararriya a shafukan sada zumunta kuma ‘yar jam’iyyar adawa ta Congress party, ta zargi sauran shafukan intanet da kai wa mata Musulmai hari tare da ikirarin suna samun goyon bayan ‘yan siyasa.

Mis Amin ta ce ba wannan ne karon farko da ake yi wa mata Musulmai haka a Indiya ba. Ko a ranar 13 ga watan Mayu lokacin da Musulmai ke bikin Salla Karama, wata tasha a shafin YouTube ta yi baje-kolin mata Musulmai a kasashen Indiya da Pakistan da aka yada kai-tsaye.

“Mutane suna tayin sayen mata daga Rufi 5 wato kasa da rabin dalar Amurka, sannan tayin ya danganta da kyan surar mace da yadda za su yi jima’i da su, kai har da barazanar yi musu fyade,” inji Mis Khan.

Mis Amin ta shaida cewa da yammacin Ranar Sallar, wani ya yi kokarin sayar da ita a Twitter, ta shafin @sullideals101, wanda daga bisani aka rufe shi. Amma kafin lokacin sun gama cin zarafin surarta. A makonnin da suka gabata, shafin Twitter ya dakatar da masu amfani da shi da ake zargin su ne suka kirkiri manhajar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Masu fafutuka sun ce matan addinai tsiraru na fuskantar cin zarafi ta shafin intanet

Masu fafutuka sun ce manufar cin zarafin mata ta shafin intanet da ake yi, ana yi ne da nufin rufewa matan baki.

A makon jiya, sama da mutum 200 daga fannoni daban-daban na duniya da suka hada da jaruman wasan kwaikwayo da mawaka da ‘yan jarida da jami’an gwamnati, sun rubuta budaddiyar wasika tare da bukatar shugabannin shafukan Facebook da Google da TikTok da Twitter su dinga bai wa mata kariyar da suke bukata.

“Intanet wani katon dandali ne na karni na 21. Waje ne da ake yin muhawara, ana saye da sayarwa, ana samar da kyakkyawan suna da bata shi. Amma yawan cin zarafin da ake yi wa mutane musamman mata ta shafukan abin ya kazanta, wannan dandali ya zama abin tsoratarwa ga mutane da dama,” a cewar wasikun.

Wani rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International kan cin zarafin mata ta intanet a Indiya a shekarar ta tagabata, ya nuna cewa matukar mace tana bayyana ra’ayinta to ba ta tsira daga wannan cin zarafi ba.

Kamar yadda mata bakar fata kan fuskanci cin zarafi a kasashen Birtaniya da Amurka, su ma matan tsirarun addinai a Indiya na samun kansu cikin wannan hali.

Nazia Erum, marubuciya kuma tsohuwar mai magana da yawun Amnesty a Indiya, ta ce akawai tsirarun mata Musulmai na kasar da ake kai wa hari.

“Irin wadannan hare-hare da ake shiryawa ana yi ne da nufin rufe bakin mata Muslmai masu ilimi, wadanda ke bayyana ra’ayinsu kan batutuwa da dama da suke nuna kin amincewa da nuna wa Musulmai kiyaya. Kokari ne na rufe bakunansu ta hanyar janyo musu abin kunya da kyama ta yadda za su yi tsit cikin al’umma,” in ji ta.

Sannan Mis Amin ta ce masu aikata cin zarafin ba sa damuwa saboda sun san babu abin da za a yi musu.

Ta kara da bayanin cin zarafi da wulakancin da aka yi wa Musulmai a baya-bayan nan, wanda magoya bayan jam’iyyar BJP mai mulki suka yi. Misali, wani minista da ya wanke mabiya addinin Hindu kan wani batanci da suka yi wa Musulmi.

Akwai kuma wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, na ministan yada labarai da ya shiga dandazon mabiya addinin hindu domin neman a harbe Musulmai.

Amma ga matan da aka wallafa sunaayensu da hotuna da sauran bayanai a manhajar “Sulli Deals” za a dauki lokaci ana kokarin ƙwato musu ‘yanci. Sai dai ba su karaya, ba sun ce sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.

”Idan ‘yan sanda ba su tsaya domin gano wadanda suka sanya hotona a manhajar ba, zan garzaya kotu, zan kuma ci gaba da bibiya ba zan karaya ba har sai na cimma nasara,” inji Mis Khan.

(BBC Hausa)

More from this stream

Recomended