Sule Lamido ya musalta janye karar da ya kai jam’iyar PDP

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yi watsi da rahoton dake cewa ya janye karar da ya shigar da jam’iyar PDP inda hakan ya share hanyar gudanar da babban taron zaben shugabannin jam’iyar da za a gudanar a Ibadan.

Lamido wanda ya karyata ikirarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a shafinsa na Facebook ya bayyana maganar da ake yadawa akan karar a matsayin labarin karya.

Tsohon gwamnan ya ce ya fara amsa kiran waya daga mambobin PDP dake fadin Najeriya bayan da ikirarin karyar da aka yi ya fara zagawa a wurin da aka shirya gudanar da babban taron a Ibadan

“Ina shawartar mambobi cewa labarin da ake alakantawa da ni ba gaskiya ba ne” ya ce .

Ya kara da cewa ” Babbar kotun tarayya yau da misalin karfe 02:30 na rana ta yanke hukunci da ya tabbatar da yancin da nake da shi na tsayawa takarar shugabancin jam’iya wanda a baya aka hana ni.”

Lamido ya ce kotun ta kuma dakatar da gudanar babban taron da aka shirya yi a Ibadan daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba har sai jam’iyar PDP ta bi matakin da kotun ta dauka.

More from this stream

Recomended