Sojojin sun lalata sansanonin yan ta’adda da dama a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar lalata sansanonin yan ta’adda da dama a jihar Borno tare da kubutar da wasu mutane 9 a wani samamame da suka kai.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi dakarun 21 Special Armoured Brigade  na rundunar Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwa jami’an tsaron Civilian JTF ne suka kai farmaki na hadin gwiwa a Geizua dake karamar hukumar Bama.

Zagazola ya bayyana cewa an kai farmakin ne a ranar Juma’a.

“Aikin farmakin kakkabe yan ta’addar ya shafi garuruwan Garin Bakura Jiga, Shehutari and Kachomri,” a cewar sadarwar.

“Yan ta’addar sun gaggauta ficewa daga sansanonin dai-dai lokacin da dakarun sojan suka tunkaro su,”

“An lalata dukkanin wasu gine-gine na yan ta’addar sojojin sun kuma gano wasu kekuna 16 inda aka lalata su nan take,”

Rahoton ya kara da cewa an kuma gano tutar yan ta’addar a sansanonin.

Mutane 8 da aka kubutar sun hada da Mata 6 da yara uku da aka yi ittifakin yayan yan ta’addan ne.

More from this stream

Recomended