Sojojin sun lalata haramtattun matatun 20 a yankin Neja Delta

Rundunar sojan Najeriya shiya ta 6 dake Fatakwal babban birnin jihar Ribas ta ce ta lalata haramtattun matatun mai 20 da a ƙalla ake tace gangan mai 20,000 tare da gano litar mai 90,000.

A wata sanarwa ranar Lahadi, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Jonah Danjuma ya ce sun kuma samu nasarar kama mutane da dama.

Ya ce an kai samame kan matatun ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro a jihohi a jihohin, Ribas, Bayelsa Delta da kuma Akwa Ibom.

“Sojoji runduna ta 6 Sojan Najeriya tare da gwiwar sauran hukumomin tsaro na cigaba da zafafa farmaki kan masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a yankin Neja Delta,” a cewar sanarwar.

“Ƙoƙarin ya kai ga lalata haramtattun matatun mai 20 kama ɓarayin mai 8 tare da lalata jiragen ruwa da ake amfani da su wajen aikata laifin,”

Satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta matsala ce da taƙi ci taƙi cinyewa abin da yake tilastawa manyan kamfanonin mai ficewa daga yankin su na komawa rijiyoyin mai dake da nisa a cikin teku.

More from this stream

Recomended