Sojojin Sudan na gargadin masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar na bukatar mulkin dimokradiyya
Hakkin mallakar hoto
Reuters

Masu zanga-zangar na bukatar mulkin dimokradiyya

Gwamnatin mulkin soja ta rikon kwarya a Sudan ta gargadi masu zanga-zanga da su cire shingayen da suka kafa kan hanyoyin Khartoum babban birnin kasar.

Masu zanga-zangar dai na kafa shingayen ne kan hanyar da za ta kai mutum zuwa shelkwatar rundunar sojojin kasar, inda a nan ne babban dandalin da ake gudanar da zanga-zangar ya ke.

A ranar Lahadi ne dai jagororin zanga-zangar suka bayyana yanke huldarsu da gwamnatin sojoji ta Sudan, inda suka zargi cewa tana dauke da sauran mambobin tsohuwar gwamnatin al-Bashir.

An yi zaton cewa a ranar Lahadin za a kafa majalisar hadaka tsakanin sojoji da farar hula wace farar hula za ta jagoranta, sai dai da alama ba a cimma matsaya ba tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai sojojin sun ce suna da niyyar mika mulkin ga farar hula duk da cewa za a dama da su a majalisar da za a kafa kuma sun fito karara sun bayyana cewa tsaron kasar zai ci gaba da zama karkashin ikonsu.

Shugaban riko na kasar Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan kan batun zanga-zangar ya ce ”ba za mu ci gaba da zama haka ba.”

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko masu zanga-zangar za su bi gargadin da sojojin suka yi.

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Masu zanga-zangar na ci gaba da gudanar da ita a Kartoum babban birnin Sudan

Daya daga cikin masu zanga-zangar Kawthar Hasaballah ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ”babu wanda ya isa ya kore mu daga wurarenmu, ko da kuwa sojoji ne.”

Ana ci gaba da zaman dirshen a gaban shelkwatar rundunar sojojin kasar tun 6 ga watan Afrilu, inda bayan kwanaki biyar aka hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

A yanzu haka dai shugabannin da ke jagoranatar zanga-zangar sun dakatar da tattaunawar da suke yi da sojojin kasar.

Kafin dakatar da tattaunawar, an yi zaton cewa tattaunawar ce za ta zama sanadiyar mika mulki ga farar hula a kasar.

More from this stream

Recomended