Sojojin Ruwa Sun Kama Ɓarayin Ɗanyen Man Fetur A Jihar Akwa Ibom

Rundunar sojan Ruwan Najeriya ta kama mutane 10 da ake zarginsu da aikata satar man fetur a jihar Akwa Ibom.

Rundunar ta kuma ce ta kwace ɗanyen man fetur lita 7000 daga hannun mutanen.

Madumom Ide kwamandan jirgin ruwan NNS Jubilee na rundunar sojan ruwan Najeriya shi ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Ibaka dake ƙaramar hukumar Mbo ta jihar.

Ide ya ce an yi kamen ne a ƙaramar hukumar Ikot Abasi dake jihar a ranar 28 ga watan Disambar shekarar 2023.

Kwamandan ya ƙara da cewa rundunar ta kuma kama wani jirgi da aka yiwa lakabi da Motor Tanker Queen Hansal da yake ɗauke da wani mai da ake kyautata zaton ɗanyen man fetur ne.

“Mutane 10 aka kama kaftin ɗaya da kuma sauran ma’aikata 10 kuma dukkanninsu ƴan Najeriya ne”

Ya ƙara da cewa man da suke ɗauke da shi kudinsa ya kai naira miliyan 800.

More from this stream

Recomended