
Lamarin wanda ya auku a jiya Asabar, a yayin artabun tsakanin sojojin Nijeriya da ‘yan Boko Haram din a yankin Buni Gari dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe, sojojin sun kashe ‘yan ta’addan guda 105, kamar yadda kakakin rundunar sojojin, Kanal Sagir Musa ya bayyana.