Sojojin Najeriya Sun Yi Kwanton Bauna Wa ‘Yan Boko Haram A Borno, Sun Hallaka 21

Dakarun Sojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI sun yi wa ayarin kayan aiki na Boko Haram/ISWAP kwanton bauna a Jihar Borno, inda suka kashe ‘yan ta’adda 21 a yankunan Sojiri da Kayamla.

Sojojin sun bayyana cewa sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa sama da ‘yan Boko Haram 100 sun taru a yankin domin kai hare-hare ga al’ummomin da ke kusa da kuma kai kayayyaki zuwa sansanoninsu.

A cikin wata sanarwa da Sojin Najeriya suka fitar a ranar Lahadi, sun ce bayan samun bayanan sirrin, dakarun, tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) da ‘yan sa-kai na yankin, sun tare ‘yan ta’addar da tsakar rana.

Sanarwar ta ce an gwabza fada mai tsanani, inda ‘yan ta’addar suka yi yunkurin kewaye sojojin daga baya, amma dakarun suka dakile harin tare da rinjaye a fafatawar.

Binciken da aka ci gaba da yi a dazukan yankin ya tabbatar da mutuwar ‘yan ta’adda 21, yayin da ake kyautata zaton wasu sun tsere da raunukan harbin bindiga. Kayayyakin da aka kwato sun hada da kekuna, abinci iri-iri, tufafi, kwayoyi, kayayyakin jinya, fitilu, da makamai da alburusai daban-daban.

Jami’in yada labarai na Rundunar Hadin Gwiwa a Arewa maso Gabas, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce ana ci gaba da wasu ayyuka domin tantance karin asara da kuma kwato wasu kayayyaki.

Sojojin sun bayyana cewa wannan nasara ta nuna muhimmancin ayyukan tsaro da ke dogaro da bayanan sirri wajen tarwatsa hanyoyin sadarwa da jigilar kayayyakin ‘yan ta’adda.

More from this stream

Recomended