10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeMoreSojojin Najeriya Sun Yi Hatsarin Mota A Maiduguri – AREWA News

Sojojin Najeriya Sun Yi Hatsarin Mota A Maiduguri – AREWA News

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

VOA Hausa

Sojojin Najeriya tara sun ji raunuka daban-daban bayan da daya daga cikin motocin da suke ciki ta yi hatsari a garin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwa da Darektan yada labaran rundunar sojin kasar Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Juma’a ta ce, sojojin suna kan hanyarsu ta kai daukin gaggawa ne a wani yankin garin na Maiduguri a lokacin da hatsarin ya auku.
“Tsantsi ne ya kwashe daya daga cikin motocin sojojin wacce ke dauke da bindiga, hakan ya sa ta zame ta afka gefen hanya, lamarin da ya sa motar ta yi juyin kuli-kulin-kubura.” In ji Nwachukwu.
Lamarin ya auku ne a kusa da garin Kuturu da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
“An kai sojojin tara da suka ji rauni wani asibitin soji ana ba su kulawa, amma ba a samu asarar rai ba.”
Babban hafsan sojin kasa Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya mika jajensa ga sojojin a cewar sanarwar.
“Janar Yahaya ya yaba da irin kokarin da dakarun suke nunawa wajen kai dauki, yana mai kira a gare su da su zama masu kiyayewa a duk lokacin da za su kai daukin gaggawa.
Dubban dakarun Najeriya na jibge a jihar ta Borno, inda suke yaki da mayakan Boko Haram da ISWAP.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here