Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.
Jita-jitar ta samo asali daga wani ɗan jarida da ya yi ikirarin cewa Lagbaja ya mutu sakamakon ciwon daji a mataki na uku a wani asibiti a ƙasar waje.
Duk da haka, majiyoyi daga hedkwatar sojoji sun tabbatar da cewa Lagbaja bai rasu ba, sai dai yana fama da matsanancin rashin lafiya. An bayyana cewa yana ƙasar waje don neman magani.
Sojojin Najeriya sun bayyana wannan jita-jita a matsayin “ƙarya”, duk da cewa ba a samu damar jin ta bakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ba a lokacin.