Sojojin Operation Hadin Kai sun sanar da cewa sun gano makamai da wasu kayayyaki yayin wani samamen duba bayan hare-haren sama da aka kai kan mayakan ISWAP a garuruwan Banki da Bula Yobe, a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Rahoton ya ce, a ranar 19 ga Satumba aka gudanar da wannan aikin tare da haɗin gwiwar dakarun haɗaka da kungiyar Civilian JTF. Wannan ya biyo bayan hare-haren sama da aka kai a ranar 18 ga Satumba, wanda ya yi sanadin hallaka aƙalla mayakan ISWAP 32.
Majiyar tsaro ta shaida wa mai binciken tsaro, Zagazola Makama, cewa an kaddamar da wannan aikin domin tantance irin barnar da aka yi sakamakon hare-haren sama.
Abubuwan da aka samu sun haÉ—a da akwati cike da harsasai na 12.7mm x 108mm, akwati na harsasai 7.62mm x 51mm NATO, keke guda É—aya da kuma riga mai launin kamufulaj.
Sojojin sun kuma gano wasu kaburbura a wurin, sai dai ba su samu damar shiga duk wuraren da aka kai hare-haren ba saboda yanayin ƙasa mai wahalar bi.
Sojojin Najeriya Sun Kwato Makamai Bayan Kashe Mayakan ISWAP 32 A Borno
