Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 12 a Borno, Sun Kwace Makamai

Sojojin Operation Hadin Kai tare da goyon bayan kungiyar Civilian JTF da wasu jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP guda 12 a jerin hare-haren da suka gudanar a Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, hare-haren sun gudana ne daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta a kauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura.

A Loskori Kura ne aka yi artabu mai tsanani tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan, inda aka kashe mutane 12 daga cikinsu.

Kayan da aka kwato sun hada da bindigogi AK-47 guda shida, gidan harsashi guda takwas da aka cika da harsasai, da kuma miyagun kwayoyi iri daban-daban. An kuma gano wasu daga cikin ‘yan ta’addan suna jinya sakamakon raunukan da suka samu a fada na baya.

Majiyar ta kara da cewa, wadannan hare-haren sun yi tasiri wajen dakile motsi da kayan aiki na ‘yan ta’addan a yankin.

A watannin baya-bayan nan, sojojin Najeriya sun kara kaimi wajen kai hare-haren kasa da sama a Arewa maso Gabas, musamman a dajin Sambisa, tafkin Chadi da tsaunukan Mandara, domin kawar da maboyar Boko Haram da ISWAP.

More from this stream

Recomended