Sojojin Najeriya Sun Karyata Labarin Cewa ‘Yan Bindiga Sun Kwace Makamai a Jihar Kwara

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan dakarunta a Obanla, Jihar Kwara, inda suka kwace bindigogi da harsasai.

A wata sanarwa da Lieutenant Colonel Polycarp Okoye, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojoji ta Division ta 2, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana labarin a matsayin ƙarya da kuma rahoton da aka ƙirƙira domin yaudaran jama’a.

Ya ce labarin da ake yadawa cewa an ci galaba a kan dakarun soji tare da sace bindigogin GPMG guda shida da harsasai sama da 30,000 ba gaskiya ba ne.

“A kowane lokaci ba a taba samun wani hari da aka ci galaba kan sansanin sojoji ba, kuma babu wani makami ko harsashi da ya fada hannun ‘yan ta’adda,” in ji Okoye.
“Wannan labarin an kirkire shi ne domin tayar da hankalin jama’a da kuma rage karfin gwiwar dakarunmu masu jarumtaka.”

Okoye ya ce dakarun bataliya ta 148 (Rear) suna ci gaba da samun nasarori a ayyukan kawar da ‘yan ta’adda a jihohin Kogi da Kwara.

Ya ƙara da cewa a wani kwanan nan, dakarun sun kafa sansanin bincike a kan iyakar Kwara da Ekiti, inda suka kashe ‘yan bindiga biyu kuma suka kwato bindigogin AK-47 sabbi guda biyu.

Rundunar ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labaran ƙarya, tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya da bayanai masu amfani.

More from this stream

Recomended