Sojojin Najeriya sun kai harin kwanton kan Boko Haram

Jajirtattun sojan Najeriya da suka fito daga Bataliya ta 222 dake Konduga tare da hadin gwiwar wasu manoma sun samu nasarar kai harin kwanton bauna akan yan ta’addar Boko Haram lokacin da suke sintiri akan titin Mushari-Galtimari a jihar Borno.

A wata sanarwa da hedkwatar rundunar sojan Najeriya ta fitar tace yan ta’addar sun je gonakin ne domin satar kayan abinci musamman albasa daga gonakin dake yankin.

Sanarwar ta kara da cewa an kashe dan kungiyar ta Boko Haram daya yayin kai harin ya yin da wasunsu suka tsere.

Yan ta’addar sun bar kekunansu a wurin tare da buhunan albasa da suka sata daga gonakin.

More from this stream

Recomended