Sojojin Najeriya Sun Ceto Fasinjoji 27 A Jihar Benue

Sojojin Najeriya sun kubutar da fasinjoji 27 da ‘yan bindiga suka sace a kauyen Amoda, karamar hukumar Ohimini a jihar Benue.

An samu nasarar ne bayan dakarun Operation Whirl Stroke sun kai samame a maboyar masu garkuwan inda suka yi galaba a kansu, suka kuma kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Rundunar sojoji ta ce wannan aiki na cikin manyan kokarin yaki da ta’addanci da laifuka a fadin kasar. A cewar ta, an kashe ‘yan ta’adda 15, an kama mutane 42 da ake zargi, kana kuma an kubutar da wasu mutane 30 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na kasa.

A Arewa maso Gabas, dakarun sun fatattaki mayakan Boko Haram da ISWAP a Dikwa, Gwoza, Bama, Banki da Gujba, inda suka kashe 15 daga cikinsu tare da kwace bindigogi, gurneti, abubuwan fashewa, babura da na’urorin sadarwa.

Haka zalika, an kama mutane 15 a Kaduna bisa laifin miyagun kwayoyi, wasu 25 a Bayelsa bisa zargin satar man fetur, da kuma mutum biyu a Delta. Haka nan, an lalata wuraren da ake yin fasa-kwaurin mai a jihohin Imo, Rivers da Delta.

More from this stream

Recomended