Gwamnatin ƙasar Faransa ta miƙa sansanin soja na farko ga gwamnatin ƙasar Chadi a wani ɓangare na shirinta na janye dakarunta da ƙasar Chadi baki ɗaya.
Shugaban rundunar sojan ƙasar Chadi a ranar Alhamis ya ce sansanin dake Faya-Largeau a arewacin ƙasar an miƙa musu shi kuma za su cigaba da sanar da ƴan kasar kan cigaban da ake samu game da shirin janye dakarun na Faransa daga birnin N’Djamena da kuma garin Abeche dake arewacin ƙasar.
Rundunar sojan ta ce dakarun Faransa sun baro garin a cikin motoci zuwa N’Djamena dake da nisan kilomita 780km sai dai ba a bayyana adadin yawansu ba.
Faransa na da dakarun soja da basu gaza 1000 ba a sansanoni daban-daban dake ƙasar.
“An miƙa sansanin ne kama yadda jadawalin da kuma ka’ida da aka cimma ta janye dakarun da ƙasar Chadi,”
A watan da ya gabata ne ƙasar Chadi ta kawo karshen yarjejeniyar soja da ƙasar Faransa inda sojan Faransa suka fara ficewa a ranar Juma’a kwanaki 10 bayan da jiragen yaƙin kasar suka fara ficewa.