Sojoji sun yi bore a filin jirgin saman Maiduguri

[ad_1]
An shiga rudani a filin jirgin saman Maiduguri dake jihar Borno bayan da sojoji da suka fusata suka riƙa harbin iska domin nuna kin amincewarsu da dauke su daga cikin Maiduguri.

Sojojin da suka fusata sun isa filin jirgin da misalin karfe 6:00 na yamma gabanin tura su ƙaramar hukumar Marte dake jihar.

Amma rikici ya fara ne lokacin da suka haÉ—u suka ki shiga jirgin da ya kamata ya dauke su zuwa can.

Sojojin na daga cikin soja da aka bawa horo na musamman sun bayyana cewa bayan da suka shafe shekaru huÉ—u a Maiduguri kamata ya yi a mayar da su gida wajen iyalansu amma ba a tura su inda za su fuskanci mutuwa ba.

Wani jami’i da ya sheda abinda ya faru ya ce sojojin sun gargadi manyansu da kada su zo a filin domin za su iya fuskantar harbi daga wurinsu.
[ad_2]

More News

Abdul Aziz Yari ya dauki nauyin karatun dalibai 1,700 a Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya baiwa 'yan asalin jihar 1,700 tallafin karatu a...

Ƴanbindiga sun kashe mataimakin shugaban jami’ar UDUS

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Sa’idu.Jami’ar wadda ta bayyana rasuwar...

NDLEA ta kama tan 761,000 na miyagun kwayoyi cikin shekaru 3

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi...

An saka jirage uku na  shugaban Æ™asa a kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen...