
Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta da suka fito daga runduna ta 6 sun kai farmaki kan masu satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta inda suka lalata haramtattun matatun mai 18 tare da kama wasu mutane 17.
Sojojin sun kai farmakin ne daga ranakun 17 zuwa 23 ga watan Fabrairu a jihohin Beyalsa, Delta da kuma Rivers inda aka gano litar mai 25,000 tare da lalata wasu jiragen ruwa 10.
Danjuma Jonah mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojan Najeriya shiya ta 6 shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal.
Jonah ya ce a wani samamen na daban sojoji sun kama wata mota dake ɗauke da litar mai 3000 na sata a mahadar Ogale dake kan titin Fatakwal zuwa Eket.