Sojoji sun kashe ‘yan sanda uku a Taraba | BBC Hausa

Sojojin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
others

Image caption

Sojojin sun kuma kubutar da wanda ‘yan sandan suka kama wanda ‘kasurgumin mai satar mutane ne’

Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta ce wasu sojojin kasar sun hallaka jami’anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wa wata tawagar ‘yan sandan wuta a jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yanda wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta bayyana cewa tawagar ta masu kai daukin gaggawa ce ta Intelligence Response Team (IRT).

Sanarwar ta ce tawagar tana karkashin jagorancin Felix Adolije, mataimakin sufuritanda na ‘yansanda, inda ta je jihar domin kama wani da ake kira Alhaji Hamisu, wanda ake zargi da cewa kasurgumin mai satar mutane ne.

Daga nan ne sai kawai wasu “sojoji na Najeriyar suka bude wa tawagar wuta ba kakkautawa”, kamar yadda sanarwar da ta fito daga kakakin rundunar ‘yan sandan ta kasa, Frank Mba, ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kama mutumin ne za su kai shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Jalingo lokacin da sojojin suka bude musu wuta, duk kuwa da cikakkiyar shedar da ke nuna cewa suna kan aikinsu.

Image caption

Tuni Babban-Sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin

Bayan ‘yan sandan, lamarin ya kuma rutsa da ran wani farar hula, da sufeto da kuma wasu ‘yan sandan biyu masu mukamin saja, yayin da wasu ‘yan sandan kuma da ba a bayyana yawansu ba suka samu raunuka.

Sanarwar ta ce bayan nan ne sai sojojin suka “kubutar da wanda ake zargin”, abin da ya sa ya tsere, har yanzu ba a san inda yake ba.

‘Yan sandan suna zargin mutumin, Alhaji Hamisu da kasancewa kasurgumin mai satar mutane, da suka dade suna nema saboda hannu a sace-sacen jama, ciki har na sace wani dan kasuwa mai harkar mai da aka yi kwanan nan a jihar ta Taraba.

Dan kasuwar mai sayar da mai wanda ba a bayyana sunansa ba a sanarwar, an ce sai da ya biya naira miliyan 100 aka sako shi.

Tuni aka tura wani mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda domin tsara yadda za a yi wa wadanda aka jikkata magani, yayin da kuma aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a asibiti.

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa Muhammad Adamu ya bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, in ji kakakin rundunar ta kasa Mista Frank Mba, mai mukamin mataimakin kwaminishinan ‘yan sanda.

Sai dai kuma babu wani martani kawo yanzu daga hukumomin sojin Najeriyar dangane da zargin na ‘yan sanda.

More from this stream

Recomended