Sojoji ‘sun kashe ‘yan bindiga da ɓarayin shanu 70’ a Kaduna

...
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ‘yan ƙato da gora sun kashe ‘yan bindiga da ɓarayin shanu 70 a dajin Kachia da ke jihar Kaduna.

Hedikiwatar tsaron Najeriya ce ta tabbatar da hakan inda ta ce rundunonin Operation THUNDER STRIKE da kuma Operation ACCORD ne suka kai wa ɓarayin farmaki bayan sun samu bayanai na sirri kan takamaiman wurin zamansu.
Hedikwatar tsaron ta tabbatar da cewa an kashe ɓarayi 70, wasu kuma sun samu tserewa da raunuka. Sojojin sun bi ɓarayin ta cikin ƙauyen Gidan Maikeri da ke dajin ƙaramar hukumar Chikun domin su fatattake su, sa’annan kuma daga baya jiragen yaƙi suka far wa ɓarayin.
‘Yan bindiga da ɓarayin shanu sun daɗe suna amfani da dajin a matsayin mabuyarsu, in ji sojojin.
Sojojin sun kuma yi kira ga mazauna yankin da su bayar da rahoto kan waɗanda aka gani da raunuka da a jikinsu musamman idan suna da alamun zargi a tattare da su.
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kai hare-hare musamman yankin Birnin Gwari.
Haka zalika a kwanakin baya sai da hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarko ga matafiya sakamakon yawaitar ɗauki ɗai-ɗai da ɓarayin ke yi wa mutane. Hakan ya tilasta wa jama’a da dama suka koma bin jigin ƙasa.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...